Mutanen Kano na goyon bayan Tinubu a zaben 2027–Sanata Barau

0
28
Jibrin-Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya bayyana cewa mutanen Jihar Kano suna da niyyar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027, bisa la’akari da irin kulawa da tallafin da yake bai wa jihar.

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake sanar da bayar da guraben karatu ga ɗaliban jami’a daga mazabarsa a Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule, Kano.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta nuna ƙoƙari wajen inganta rayuwar al’umma a Kano, inda ya ambaci misalai kamar haɓaka Kwalejin Ilimi ta Tarayya zuwa cikakkiyar jami’a da kuma sauya mata suna don girmama marigayi Yusuf Maitama Sule. Haka kuma, ya ce an mayar da Kabo Polytechnic jami’a wani abu da aka daɗe ana nema amma yanzu ya samu nasara da taimakon Shugaba Tinubu.

Haka zalika, ƙaramin ministan gidaje  Abdullahi Atta, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe Naira biliyan 200 domin gina layin dogo mai amfani da hasken lantarki daga Kaduna zuwa Kano, inda ake sa ran fara aikin sa nan ba da jimawa ba.

Sanata Barau ya ce mutanen Kano suna jin daɗin irin goyon bayan da Shugaba Tinubu ke ba su, kuma suna shirye-shiryen nuna godiyarsu ta hanyar sake zaben sa a shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here