Matatar Dangote ta yaba wa Tinubu akan yajin aikin PENGASSAN

0
39

Matatar man fetur ta bayyana cewa yajin aikin ƙungiyar PENGASSAN bai kawo cikas ga ayyukanta ko na ɗan lokaci ba, duk da tsawon kwanaki biyu da yajin ya ɗauka.

Matatar ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin sa na X inda ta gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran jami’an gwamnati bisa rawar da suka taka wajen kawo ƙarshen yajin aikin.

> “ Matatar Dangote na godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ministoci da jami’an tsaro bisa matakan da suka ɗauka wajen dakile cikas da yajin aikin PENGASSAN zai iya haifarwa,” in ji sanarwar.

Kamfanin ya ƙara da cewa yana yaba wa ‘yan Najeriya bisa goyon bayansu, yana mai cewa kamfanin Dangote shi ne babban mai ba da aikin yi na musamman da kuma mai biyan haraji mafi girma a ƙasar nan.

A baya, ƙungiyar PENGASSAN ta shiga yajin aiki ne bisa zargin sallamar ma’aikata da kamfanin ya yi, sai dai bayan shiga tsakani na gwamnati, an cimma matsaya ta fahimtar juna cikin kwanaki biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here