Kotu ta aike da ɗan TikTok Mai-wushirya, zuwa gidan hali, bisa zargin wallafa hotunan rashin tarbiyya tsakanin sa da wata Wada.Kotun majistare mai lanba 7 dake jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Halima Wali, ce ta aike da Maiwushirya zuwa Gidan gyaran halin, bayan da rundunar Hisbah ta Kano, ta kama shi a kwanakin baya.
Ana dai zargin sa da aikata abubuwan da suka saɓa wa tarbiyyar Muslunci.