Gwamnan Bauchi ya nemi yafiyar mutanen da ya cutar

0
20

Gwamnan Bauchi ya nemi yafiyar mutanen da ya cutar

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya cika shekara 67 a ranar Litinin, inda ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa cikin neman gafara daga duk wanda ya taɓa cuta a rayuwarsa ta siyasa da mulki.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamnan ya gode wa Allah bisa rahama da jagoranci a duk tafiyarsa ta rayuwa da shugabanci. Ya ce wannan rana ce ta tunani da godiya, ba ta shagali ba.

Bala Mohammed ya tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da mulki bisa adalci, gaskiya da tausayi, tare da gina al’umma mai ci gaba.

Ya gode wa iyalinsa, abokai da al’ummar Bauchi bisa addu’o’i da goyon bayan da suke masa, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali kan ilimi, lafiya da inganta ababen more rayuwa.

Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da zaman lafiya da haɗin kai don cigaban Bauchi da Najeriya baki ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here