Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa aƙalla mutane 4,778 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar kwalara tsakanin shekarar 2020 da 2024.
Rahoton hukumar ya nuna cewa a shekarar 2020 an yi zaton mutane 3,513 ne suka kamu da cutar, inda 95 daga cikinsu suka mutu. Sai dai a shekarar 2021 an samu ƙaruwa sosai, inda mutane 111,062 aka yi zaton sun kamu da cutar a jihohi 33, kuma 3,604 daga cikinsu suka mutu.
A shekarar 2025 ma, cutar ta ci gaba da kamari, inda fiye da mutane 300 suka mutu. Cikin wannan adadi har da mutum 179 da gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwarsu daga cikin mutum 12,052 da ake zargin sun kamu da cutar a watan Satumba kaɗai.
Haka kuma, mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tabbatar da mutuwar mutum 58 cikin sabbin masu kamuwa 258 da aka gano a ƙananan hukumomi 14 na jihar — kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wannan matsala na faruwa ne duk da cewa Najeriya ta samu tallafi daga babban bankin duniya domin samar da tsaftataccen ruwa da muhalli, tare da ƙarin tallafin dala miliyan biyu daga Majalisar Ɗinkin Duniya don rigakafin kwalara.