Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, ya bayyana cewa tashin farashin gas na girki da ake fuskanta a ƙasar nan ya samo asali ne daga yajin aikin ƙungiyar ma’aikatan man fetur (PENGASSAN).
Babban daraktan kamfanin, Bayo Ojulari, ne ya bayyana haka yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati.
A cewar Ojulari, yajin aikin ya haifar da tsaiko wajen jigilar kayayyaki, wanda ya janyo ƙarancin gas a kasuwa, sannan wasu dillalai suka yi amfani da hakan wajen ƙara farashi.
> “Tashin farashin ya zama kamar na wucin gadi. Da zarar an kammala dawo da harkokin jigila yadda ya kamata, farashin zai dawo yadda yake a da,” in ji Ojulari.
Rahotanni sun nuna cewa a Lagos, kg ɗaya na gas ya kai ₦2,080, inda 12.5kg ke sayuwa a ₦26,000, yayin da a Iyana Ipaja ya kai ₦27,000.
A Abuja kuma, farashin ya tashi zuwa ₦20,000 don 12.5kg, wanda ke nufin ₦1,600/kg — ƙaruwa da fiye da kashi 48% daga tsohon farashin ₦17,500.
NNPC ta tabbatar da cewa yanzu da yajin aikin ya ƙare, farashin zai ragu a hankali yayin da dillalai ke ci gaba da karɓar sabon kaya daga cibiyoyin ajiya.
A ranar 1 ga Oktoba, ƙungiyar PENGASSAN ta dakatar da yajin aikin da ta shirya bayan sulhu da gwamnatin tarayya da kamfanin Dangote Refinery, inda aka amince da dawo da ma’aikatan da aka sallama.