Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kaddamar da sabon bincike kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan 4 na kuɗin jihar zuwa aikin tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port, wanda ake zargin ya faru a zamanin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Rahotanni sun nuna cewa kuɗin da aka karkatar an yi amfani da su ne wajen bayar da kwangilar gina wasu muhimman abubuwan more rayuwa a wurin aikin tashar, duk da cewa a wancan lokaci an riga an cire hannun jihar daga cikin masu hannun jari a kamfanin.
Rahotonni sun ce a shekarar 2020, an maida kaso na hannun jari na jihar (kashi 20%) zuwa cikin mallakar iyalan tsohon gwamnan Kano Ganduje, inda ƴaƴan Ganduje suka zama daraktoci da masu hannun jari a tashar.
Majiyoyi sun tabbatar cewa hukumar PCACC ta fara binciken ne bayan karɓar ƙorafe-ƙorafe daga jama’a kan yadda kuɗin jihar suka bace ba tare da izini ba.
Shugaban hukumar, Saidu Yahya, ya tabbatar da ci gaban binciken a hirar da ya yi da SolaceBase a karshen mako.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu nan ba da jimawa ba, domin an samu hujjoji m da ke tabbatar da laifin karkatar da kuɗin jihar Kano.