Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 5.397 domin gyaran makarantar Government Day Science College, da wasu makarantun gwamnati a fadin jihar.
Hakan na zuwa ne bayan wani fitaccen mai amfani kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci (Dan Bello), ya wallafa bidiyo da ke nuna halin rashin gyara da makarantar ke ciki, wanda ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gani da ido.
Daga cikin kudaden da aka amince da su, an ware Naira miliyan 905 don gyaran Day Science College, Naira miliyan 397 don GSS Rimi a Sumaila, da Naira biliyan 1.4 don GTC Kofar Nassarawa.
Haka kuma, Naira miliyan 546 za a yi amfani da su wajen gyaran kwalejin noma ta Audu Bako a Dambatta, yayin da Naira biliyan 1.8 za a kashe ta don gyaran makarantu a kananan hukumomi 44 na jihar.