Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan 288.6 wajen gyaran babban masallacin Juma’a na Kano.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a ranar Juma’a.
A cewarsa, majalisar ta kuma amince a yi gyaran makarantar sakandire ta Government Technical College (GTC) akan kudi Naira biliyan 1.46.
Kwamishinan ya ce matakan gyaran na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na farfaɗo da muhimman wuraren tarihi da ilimi a fadin jihar.