Gwamnatin Kano Ta Gargaɗi Malamai Daga Wajen Jihar Kan Binciken Malam Triumph

0
59

Gwamnatin Kano Ta Gargaɗi Malamai Daga Wajen Jihar Kan Binciken Malam Triumph

Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗi ga wasu malamai daga wajen jihar da su guji yin magana ko sharhi da zai iya kawo cikas ga binciken da kwamitin shura ke gudanarwa kan zargin da ake yi wa Malam Lawan Abubakar Shu’aibu Triumph, a kan cin zarafin Annabi Muhammad (SAW).

Sakataren kwamitin, kuma Kwamishinan Kasuwanci na jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kano.

Sagagi ya ce gwamnati ta lura da yadda wasu malamai daga wasu jihohi ke tsoma baki cikin batun kafin kammala binciken, abin da ya bayyana a matsayin abu da zai iya kawo tangarda ga aikin kwamitin da ke tafiya bisa gaskiya da adalci.

Ya tabbatar da cewa kwamitin zai ci gaba da aikinsa ba tare da tsangwama daga kowa ba, tare da tabbatar da cewa sakamakon binciken zai fito bisa gaskiya da bin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here