Fitaccen Ɗan Jarida a Kano Aliyu Abubakar Getso, ya Rasu

0
39

Rahotanni sun tabbatar da cewa fitaccen ɗan jarida Malam Aliyu Abubakar Getso, ya rasu da safiyar Lahadi bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Malam Getso, wanda aka fi sani da Baba Getso, ya yi aiki a kafafen yada labarai da dama a jihar Kano — ciki har da na gwamnati da kuma masu zaman kansu — inda ya taka rawar gani wajen aikin jarida.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya karɓi kyawawan aikinsa, ya kuma sanya shi cikin rahamar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here