An samu sabon tarihin hauhawar kasuwar crypto, inda darajar kowane Bitcoin ɗaya ta kai farashin dala $125,000 a safiyar Lahadi, wanda ya zama mafi girma tun bayan samar da kasuwar crypto.
Wannan hauhawar na nufin karin kusan kashi 97 cikin 100 daga farashin dala $62,000 da aka samu a watan Oktoba na shekarar 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa hauhawar ta samu ne sakamakon sabbin dokoki masu kyau da kuma tashin darajar hannayen jari a Amurka, inda manyan kasuwanni kamar S&P 500 da Nasdaq suka samu tagomashi.
A cewar CoinMarketCap, a karfe 8:55 na safe ranar Lahadi, farashin Bitcoin ya tsaya a dala $124,913, yayin da Ethereum, ya tashi da kashi 2.4% zuwa dala $4,609.
Tun farkon wannan shekara, darajar Bitcoin ta rika karuwa sosai, sakamakon sabon tsarin dokoki da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka ta samar, wanda ke goyon bayan masana’antar kuɗin internet.