Shugaban jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), Farfesa Adamu Ahmed, ya bayyana cewa jami’ar tana kashe sama da Naira biliyan 4 a kowace shekara wajen samar da wutar lantarki a jami’ar abin da yace ba mai dorewa ba.
Yayin bikin cika shekara 63 da kafuwar jami’ar, Farfesan ya ce gwamnati ta tallafa da Naira biliyan 1 ta hannun TETFund, tare da amincewa da sabon aikin samar da wuta mai amfani da hasken rana mai ƙarfin megawatt 10.
Ya ƙara da cewa tsoffin ɗalibai da jami’ar suna haɗa kai wajen samar da makamashi mai dorewa, musamman ta hanyar ayyukan hasken rana.
ABU, wadda aka kafa a 1962, ta samu matsayi na jami’ar gwamnati mafi inganci a Najeriya a 2025, kuma tana cikin manyan jami’o’i uku da suka fi daraja a ƙasar nan.