Ƴan bindiga sun kashe likita da sace ƴaƴan sa a Abuja

0
44

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wani likitan dabbobi da ke Abuja, Dr. Ifeanyi Ogbu, tare da sace ‘ya’yansa uku a unguwar Kubwa da ke babban birnin tarayya.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai farmaki gidan likitan da ke kan titin Kubwa–Kaduna da yammacin Juma’a, inda suka yi awon gaba da shi da ‘ya’yansa uku. Bayan wani lokaci sai aka gano gawarsa a gefen hanya, yayin da yaran har yanzu suke hannun masu garkuwa.

Andrew Gabriel Ikechukwu, wanda ya tabbatar da rasuwar Dr. Ogbu ta shafinsa na Facebook, ya rubuta cewa:

> “Dr. Ifeanyi Ogbu, tsohon shugaban ƙungiyar likitocin dabbobi ta yankin FCT, wanda aka yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa uku, an samu gawarsa a gefen hanya. ‘Ya’yansa kuwa har yanzu ba a sako su ba. Allah Ya taimaka.”

Marigayin ya kasance gogaggen likitan dabbobi kuma tsohon shugaban ƙungiyar likitocin dabbobi ta Abuja. Ya bar mata mai jinya da iyali masu alhini.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan Abuja ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba, sai dai majiyoyi sun tabbatar cewa bincike yana gudana domin gano masu hannu a harin da kuma ceto yaran da aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here