Rahotanni daga Mashegu, Jihar Neja, sun bayyana cewa ’yan bindiga sun tilasta wa al’ummomin yankunan Babban Rami, Kaboji, Sabon Rijiya da wasu ƙauyuka biyan haraji da ya kai Naira miliyan 10 gaba ɗaya.
Wasu mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun kashe mutane da dama tare da ci gaba da kai hare-hare, musamman a gonakin da ke kusa da dazukan Ibbi da gandun dabbobi na Kanji National Park.
Mutanen sun roƙi gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakin tsaro don kare rayukan manoma, inda suka bayyana cewa yawancinsu ba su ma kai girbi ba kafin hare-haren su fara.
Rundunar ’yan sanda ta Jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa yanzu.