Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa a lokacin mulkinsa, kungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari domin jagorantar tattaunawa tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
Jonathan ya bayyana haka ne a Abuja, yayin kaddamar da littafi mai suna “Scars”, wanda tsohon shugaban rundunar sojoji, Janar Lucky Irabor, ya rubuta.
A cewar Jonathan, “Ɗaya daga cikin kwamiti da muka kafa a wancan lokaci, Boko Haram ta nemi Buhari domin ya wakilce su wajen tattaunawa da gwamnati.”
Sai dai tsohon kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya karyata wannan ikirari, yana mai cewa wannan magana “ƙarya ce kuma tana da nasaba da siyasa.”
> “Idan wannan wani ɓangare ne na shirinsa na neman shugabanci a 2027, to muna so mu faɗa masa cewa ya fara da ƙarya,” in ji Shehu.
Shehu ya ce babu wani lokaci da marigayi Muhammad Yusuf ko Abubakar Shekau — tsoffin shugabannin kungiyar Boko Haram — suka taɓa ambaton Buhari a matsayin wanda za su so ya shiga tattaunawa da su.
Ya ƙara da cewa Shekau ma har ma ya taɓa yin barazana ga Buhari, inda ya yi ƙoƙarin kai masa hari da bam a Kaduna a shekarar 2014.
Shehu ya tuna da kalaman Buba Galadima, tsohon sakataren jam’iyyar CPC, wanda ya taɓa cewa rahoton cewa Boko Haram ta naɗa Buhari “tatsuniya ce kawai”.
A ƙarshe, Shehu ya shawarci Jonathan da ya “nemo wani labari mafi kyau” idan yana neman dawowa siyasa kafin 2027.