Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa wasu kafafen yada labarai sun sauya ma’anar kalamansa da ya yi game da marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan batun Boko Haram.
Jonathan ya yi wannan bayani ne yayin bikin ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, inda ya bayyana cewa ƙungiyar Boko Haram ta taɓa ambaton Buhari a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da take son su shiga tsakani a tattaunawa tsakaninta da gwamnatin tarayya a lokacin mulkinsa.
Sai dai Garba Shehu, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, ya musanta wannan batu, yana mai cewa wani ɓangare ne na ƙungiyar ya yi wannan magana “wanda ma Buhari kansa bai san da shi ba.”
A wata sanarwa da mai magana da yawun Jonathan, Ikechukwu Eze, ya fitar a yammacin Asabar, ya ce kalaman Jonathan an fassara su ba daidai ba, domin dai tsohon shugaban bai yi nufin cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba, sai dai kawai yana misalta dabarun da ƙungiyar ta dinga amfani da su a wancan lokaci.
> “Jonathan bai faɗi hakan don ya nuna cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ko yana goyon bayan su ba, sai dai don ya fayyace irin dabarun da ƙungiyar ke amfani da su wajen yaudarar jama’a,” in ji sanarwar.