Akwai yiwuwar Tinubu zai saki Nnamdi Kanu–Gwamnan Abia

0
28

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu yana da niyyar ganin cewa shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya samu ‘yanci a nan gaba kadan.

Otti ya bayyana haka ne yayin ziyarar aiki ta yini guda da shugaban ƙasa ya kai jihar, ta hannun Ministan Ayyuka, Dave Umahi.

Gwamnan ya ce: “Ina tattaunawa da shugaban ƙasa a kan batun Nnamdi Kanu, kuma yana da kyakkyawar niyya a kai. Ina tabbatar muku cewa ba da jimawa ba, Kanu zai samu ‘yanci.”

Ya ƙara da cewa dangantakarsa da Tinubu ta daɗe, kuma yana da tabbacin shugaban ƙasa zai cika alkawarinsa.

A nasa ɓangaren, Minista Umahi ya roƙi mutanen Kudu maso Gabas da su ci gaba da zama cikin haɗin kai da zaman lafiya.

Tun daga shekarar 2021 ake tsare da Nnamdi Kanu a hannun hukumar DSS bayan an kama shi daga Kenya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here