’Yan Sandan Kano Sun Gurfanar da Mutanen Da Ake Zargi Da Fashi Da Makami

0
47

Rundunar ’yan sanda ta gurfanar da wasu mutane biyar a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a, Alkali Ibrahim Sarki Yola.

Mutanen da ake tuhuma sun haɗa da Yusif Yahaya, Zahraddeen, Abdullahi, Kamalu da Mubarak.

Lauyan gwamnati, Barista Nafiu Minjibir, shi ne ya gabatar da ƙarar a gaban kotun.

A cewar tuhumar, ana zargin waɗannan mutum biyar da haɗa kai wajen aikata fashi da makami a unguwar Sabuwar Gandu, inda suka tare wasu jama’a da ke zaune a kofar gida tare da yi musu fashi.

Lokacin da aka karanta musu tuhumar, dukkan su sun amsa laifin sai dai Zahraddeen ya musanta aikata laifin.

Kotun ta bukaci a gabatar da shaidu a zaman gaba domin ci gaba da sauraron ƙarar, tare da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here