Kotu ta Dakatar da ‘Yan Sanda Daga Tilasta Bin Dokar Lasisin Gilashin Mota Mai Duhu

0
58

Babbar Kotun Tarayya da ke Warri, Jihar Delta, ta bayar da umarni ga Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da su dakatar da tilasta bin dokar lasisin gilashin mota mai duhu (tinted glass permit).

Wannan umarni ya fito ne bayan wani lauya, John Aikpokpo-Martins, ya shigar da ƙara yana kalubalantar ingancin tsarin da ‘yan sanda suka dawo da shi ta hanyar dandalin su na intanet (POSSAP).

A watan Yuni 2025 ne aka fara aiwatar da wannan doka bayan wa’adin kwanaki 30, inda daga baya aka ƙara wa’adin sau biyu – daga watan Agusta zuwa watan Oktoba – domin bai wa masu ababen hawa lokaci su yi rajista. Hukumar ‘Yan Sanda ta kare wannan mataki da hujjar tsaro, tana mai cewa masu laifi na amfani da motocin da aka yi musu gilashi mai duhu wajen gujewa gano su.

Sai dai masu sukar dokar sun ce wannan mataki na tauye ‘yancin sirri da ‘yancin motsi na ‘yan ƙasa, tare da ƙara haifar da cikas da cin zarafi daga jami’an tsaro a hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here