Gobarar Tankar Mai Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane da Dama a Jihar Ogun

0
43

Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wata tankar mai cike da fetur ta kife tare da haddasa gobara a kan hanyar Abeokuta–Sagamu da ke jihar Ogun, a safiyar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa tankar ta kife ne a gefen hanya inda ta zubar da man fetur, wanda daga bisani ya haddasa gobara a kan hanyar Abeokuta–Kobape–Siun–Sagamu.

Mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirga ta jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, inda ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da kima da kuma rashin iya sarrafa motar daga direban.

Ya bayyana cewa gobarar ta ƙone manyan tirela da ƙarin wata mota, tare da lalata wayoyin wuta da ke baiwa garin Mowe da kewaye hasken lantarki.

Akinbiyi ya ce, “Yanzu haka ba a iya tantance adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ba, amma jami’an ceto daga TRACE, hukumar kashe gobara ta jihar Ogun, hukumar FRSC, Nestlé PLC Fire Service da kuma ’yan sanda na ci gaba da aikin kashe gobara da kuma tabbatar da tsaro.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here