An samu tashin gobara a ɗaya daga cikin gidajen kwana na ɗalibai mata a Jami’ar Gombe a daren Alhamis.
Gobarar ta tashi ne a misalin ƙarfe 9:30 na dare, lamarin da ya tilasta ɗalibai su fice da gaggawa domin tsira da rayukansu, inda suka bar dukiyoyinsu a cikin ɗaki.
Shaidu sun bayyana cewa dalibai maza da mata sun yi ƙoƙarin kashe gobarar kafin isowar jami’an kashe gobara. Duk da haka, an ruwaito cewa an yi asarar kayan ɗalibai da dama, duk da cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya samu munanan raunuka.
Mai magana da yawun jami’ar, Hadu Ligari, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa an ɗauki matakan gaggawa kuma an shawo kan gobarar. Ya ƙara da cewa hukumar jami’ar tana bincike kan musabbabin gobarar da kuma asarar da aka yi.
Wata majiya daga jami’ar ta bayyana cewa gobarar na iya zama ta samo asali ne daga amfani da gas a cikin ɗakunan kwanan ɗalibai. Rahotanni sun nuna cewa kwanan nan jami’ar ta janye takunkumin amfani da kwalaben gas a gidajen kwana.