Da baƙin cikin satar ɗaliban makarantar Chibok zan mutu—Jonathan

0
70

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa satar ’yan matan makarantar sakandaren Chibok da Boko Haram ta yi a shekarar 2014 ya kasance mummunan rauni da zai kasance da shi har ƙarshen rayuwarsa.

Jonathan ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” da tsohon shugaban hafsoshin tsaro na ƙasa, Lucky Irabor, ya rubuta.

Ya ce wannan lamari ba zai taɓa gogewa daga tunaninsa ba. Jonathan ya kuma bayyana cewa a lokacin da gwamnatinsa ke ƙoƙarin tattaunawa da Boko Haram, ƙungiyar ta zaɓi Muhammadu Buhari — wanda daga baya ya gaje shi a 2015 — a matsayin wanda za su fi so ya wakilce su wajen sulhu da gwamnati.

“Lokacin da suka zaɓi Buhari a matsayin wakilinsu, na yi tsammanin idan ya hau mulki zai yi sauƙi a tattauna da su su miƙa makamai. Amma har yanzu Boko Haram tana nan,” in ji shi.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce gazawar gwamnatin Buhari wajen kawo ƙarshen rikicin ya nuna cewa lamarin Boko Haram ya fi rikitarwa fiye da yadda ake tsammani.

Jonathan ya tunatar cewa rikicin Boko Haram ya fara ne tun 2009, lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa ga marigayi Umaru Musa Yar’Adua. Ya ce daga lokacin da ya hau mulki a 2010, ya shafe shekaru biyar yana fafatawa da ƙungiyar har zuwa ƙarshen wa’adinsa.

“Ina ganin cewa bayan na bar mulki, Buhari zai iya murkushe su cikin gajeren lokaci. Amma har yanzu suna nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here