Rahotanni sun ruwaito cewa an dakatar da Sheikh Abubakar Lawal Shua’ibu Triumph daga yin karatu a Jihar Kano, lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mabiyansa da al’umma.
Sai dai ɗaya daga cikin makaman Izala Barista Ishaq Adam Ishaq ya fito fili ya karyata wannan ikirari, inda ya bayyana cewa Sheikh Triumph ba’a taɓa dakatar da malamin daga gabatar da karatu ba.
A cewar Baristan, abin da aka tattauna kawai shi ne a guji magana kan wasu al’amuran da ke cikin dambarwar Malam Lawan da waɗanda suka kai ƙorafi akan sa kan zargin cin zarafin Annabi Muhammad SAW, amma hakan bai shafi sauran karatuttukan malamin ba.
Barista Ishaq ya jaddada cewa karatu da wa’azi haƙƙi ne na kowane ɗan adam, kuma babu wanda zai iya hana Sheikh Lawal ci gaba da gudanar da darussan da ya saba kamar Umadatul Ahkam, Jawahirul Ma’ani, Tafsiri da Riyadussalihin.
Duk da ce-ce-ku-cen da ake yi, Sheikh Triumph ya ci gaba da gabatar da darussa ta kafafen sada zumunta, abin da ya tabbatar da cewa ba a katse masa karatu ba.


