’Yan bindiga sun ƙwace wayoyin ƴan sanda, sace Kansiloli da Liman a Zamfara

0
72

 

A wani hari da ya tayar da hankali, ’yan bindiga sun kai farmaki a unguwar Tsauni da ke cikin Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda suka sace wasu kansiloli biyu tare da wani liman.

Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Sanusi Gama Giwa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa kansilolin da aka sace ’yan majalisar ƙaramar hukumar Maradun ne.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama kansilolin ne da misalin ƙarfe 8:05 na dare, jim kaɗan bayan sun idar da sallah a wani masallaci da ke kusa da ofishin ’yan sanda. Waɗanda suka shiga hannun ’yan bindigar sun haɗa da kansilolin da ke wakiltar mazaɓun Gidan Goga da Tsibiri.

Shaidu sun ce maharan sun kuma kwace wayoyin salula daga hannun wasu ’yan sanda da suka kasance a wajen, kafin su tsere da mutanen da suka kama.

Ya zuwa yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan matakan da ake ɗauka ba, yayin da al’ummar yankin ke ci gaba da rayuwa cikin tsoro da fargaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here