Wata mata ta bankawa kanta wuta, ta rasu a jihar Bauchi

0
49

Wani mummunan lamari ya faru a jihar Bauchi, inda wata mata da ake kyautata zaton tana da matsalar tabin hankali ta banka wa kanta wuta a gidan tsohon Fira Ministan Najeriya, Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Shaidu sun bayyana cewa matar – ‘yar wani tsohon alkalin kotun shari’a a jihar ce, ta zo gidan ne a keke Napep dauke da galan na man fetur. Bayan ta tambayi ‘yar Balewa, Hajiya Yelwa Abubakar Balewa, wadda ita ce shugabar hukumar kula da marayu da marasa galihu ta Bauchi (BASOVCA), aka shaida mata ba ta nan. Nan take sai ta zuba man a jikinta ta banka wa kanta wuta a bakin ƙofar gidan.

An garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda likitoci suka yi ƙoƙarin ceton ranta, amma daga bisani ta rasu sakamakon munanar ƙonewa da tayi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin. Kakakin rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana shi a matsayin abin takaici ƙwarai, tare da sanar da cewa kwamishinan ‘yan sanda ya umarci gudanar da bincike mai zurfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here