Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Taraba, sun kwace makaman ɓata gari

0
42

Sojojin rundunar 6 Brigade na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun yi nasarar hana wani harin ’yan ta’adda a jihar Taraba.

Wani jawabi da Umar Muhammad, mai rikon mukamin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ya fitar a Jalingo ya bayyana cewa dakarun sun yi aiki bisa sahihan bayanan sirri da suka samu, inda suka sauka a kauyen Tor-Ikyeghgba a ranar 1 ga Oktoba 2025.

A cewar sa, da isar su yankin, sojojin sun gamu da ’yan ta’addan a kusa da wani layin wutar lantarki, inda aka yi musayar wuta tare da samun nasarar kashe biyu daga ƴan ta’addan.

Dakarun sun kuma kwato bindigogi, harsasai, rediyo, babur, da wasu kayan more rayuwa.

Kwamandan rundunar, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya jinjinawa sojojin bisa jajircewarsu da gaggawar kai dauki. Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Taraba.

Haka kuma ya roƙi al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa a yaki da ta’addanci da ayyukan taɓarɓarewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here