Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci gwamnati ta dauki matakan sauye-sauye masu muhimmanci domin ƙara wa mata dama a jagoranci, fannoni daban-daban na siyasa da tattalin arzikin ƙasar nan.
Sanusi ya yi wannan kira ne a yayin wani taron musamman da aka gudanar a birnin Legas kan harkokin da suka shafi daidaita jinsi da samar da cigaba mai ɗorewa.
Sarkin wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ne ya bayyana cewa ya kamata batun daidaita jinsi a rika kallonsa a matsayin abu na adalci da hikima, ba wai taimako na alfarma ba. Ya ce shingen da ake kafa wa mata wajen shiga mukaman jagoranci ana ƙirƙiro su ne ko kuma ana ƙarfafa su da gangan, don haka wajibi ne a rushe su.
Ya kuma bukaci a yi gyaran kundin tsarin mulki domin samar da tanadi na musamman da zai baiwa mata kaso mai tsoka a mukaman gwamnati, ciki har da kaso 30 zuwa 40 cikin ɗari na ministoci, ko kuma tsarin juyawa a kujerun majalisar dattawa domin ƙara wakilcin mata.
A nasa jawabin, Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Geoffrey, ya tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa cigaban tattalin arzikin da mata za su fi amfana da shi.