Murtala Sule Garo Ya Taya Abubakar Kabir Bichi Murnar Cika Shekaru 44

0
38

Ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Murtala Sule Garo, ya taya murna ga ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bichi, kuma shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai, Engr. Abubakar Kabir Bichi, bisa cika shekaru 44 da haihuwa.

A cikin saƙon da ya fitar a ranar Laraba, Garo ya bayyana Bichi a matsayin shugaba nagari, mai jajircewa da hangen nesa, wanda ya zama abin koyi ga matasa da sauran ’yan siyasa.

Garo ya ce Abubakar Bichi ya tabbatar da irin rawar da matasa za su iya takawa a shugabanci idan aka ba su dama, inda ya yabawa gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

> “Cikin farin ciki nake miƙa sakon taya murna a wannan rana ta musamman, wacce ka cika shekaru 44 cikin jajircewa da ƙoƙarinka na hidima ga jihar Kano da ƙasarmu Najeriya. Hakika Bichi ya zama abin koyi a wurin matasa da ’yan siyasa. Ina roƙon Allah ya cigaba da yi maka jagora,” in ji shi.

Ya kuma yi fatan Allah ya ƙara wa Bichi shekaru masu albarka da nasarori a rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here