Likita ɗaya ne yake duba lafiyar mutane 9,083, Najeriya—NARD
Ƙungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta ƙasa (NARD) ta bayyana damuwa kan matsalar ƙarancin likitoci a ƙasar nan, inda ta ce yanzu likita guda ɗaya ne ke kula da marasa lafiya 9,083.
Wannan adadi, in ji ƙungiyar, ya saɓa da ƙa’idar aikin lafiya a duniya.
A cikin sanarwar da ta fitar yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, ƙungiyar ta sanar da cewa ya kamata a samar da mafita akan karancin likitoci.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Mohammad Suleiman, ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga yawan barin ƙasar da likitoci ke yi, inda fiye da 16,000 suka yi hijira cikin shekaru bakwai da suka gabata. A halin yanzu, ƙasar na da kusan likitoci 11,000 kacal da ke yi wa al’ummar da suka kai miliyan 240 hidima.
Wannan ya jefa likitoci cikin aiki mai nauyi, inda wasu ke shafe sama da awanni 106 suna yin aiki a mako ɗaya.
NARD ta yi gargadi cewa wannan yanayi na iya haifar da mace-macen da za’a iya kaucewa faruwar su, tare da yin kira ga Ma’aikatar Lafiya ta ƙasa da ta inganta albashi, ta sanya ƙa’idar maye gurbin likita nan take idan wani ya bar aiki, da kuma takaita yawan lokutan aiki.