Lauyoyi Mata Sun Yi Zanga-Zanga a Kano Kan Sauya Kwamishinan ‘Yan Sanda

0
55

Kungiyar mata lauyoyi a Kano ta gudanar da wata zanga-zangar lumana a kan titin Tukur Road, inda suka bukaci Babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun, da kada ya amsa kiran Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ta neman sauya Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.

Shugabar kungiyar, Barrister Nafisa Abba Isma’il, wadda ta jagoranci zanga-zangar, ta ce abin da jama’a ke bukata shi ne a kawo karshen matsalolin tsaro irin su kwacen waya, tada tarzoma daga ‘yan daba, da safarar miyagun kwayoyi, ba wai sauya kwamishinan ‘yan sanda ba. Ta jaddada cewa CP Bakori ya riga ya nuna jajircewa da bajinta wajen kare lafiyar jama’a a Kano.

A yayin zanga-zangar, mata da kungiyoyi daban-daban sun fito dauke da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce na kira ga Babban Sufeton ‘Yan sanda da kada ya yi watsi da nasarorin da aka samu karkashin shugabancin Bakori.

Masu zanga-zangar sun kuma gudanar da addu’o’i tare da yin kira da babbar murya ga Sufeton ‘Yan sanda da ya ci gaba da mara wa kwamishinan baya, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kano.

Tun da farko, yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar 1 ga Oktoba a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci a sauya CP Bakori bisa hujjar cewa baya amfani da ƙwarewar aiki. Sai dai zuwa yanzu, kwamishinan ‘yan sandan Kano bai mayar da martani kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here