Hukumar yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta sanar da kama mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jirgin saman Abuja.
Cikin waɗanda aka kama, akwai wani mutum da ya yi ƙoƙarin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. A cewar hukumar, matasan da aka kuɓutar na da shekaru tsakanin 15 zuwa 26, daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas. Ana shirin kaisu ƙasashe kamar Iraƙi, Sudan, Masar, Saudiyya, Bahrain da Afghanistan.
Babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello, ce ta jagoranci aikin bisa bayanan sirri da aka samu. Hukumar ta ce har ma akwai wani babban jami’in tsaro cikin waɗanda ake zargi.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kuɓutar ta bayyana cewa sai ta tabbatar da gurfanar da mahaifinta a kotu kan yunƙurin safararta. Wata kuma ta ce mahaifiyarta ta tilasta mata yarda ta tafi ƙasashen waje da nufin yin aiki don samun kuɗi.