Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya janye daga takarar shugabancin ƙasa a 2027 domin ya mara wa matashi baya.
A wata hira da ya yi da BBC, Atiku wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya ce har yanzu bai yanke shawarar tsayawa takara ba, amma idan matashi ya kayar da shi a zaɓen fitar da gwani, zai amince ya mara masa baya tare da ba shi cikakken goyon baya.
“Idan na tsaya, matashi ya kayar da ni, to shi kenan, zan karɓa. Kuma zan taimaka masa da ilimin siyasa da gogewa,” in ji shi.
A watan Yulin 2025, Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP saboda sabanin ra’ayi, inda ya jagoranci wasu manyan ‘yan adawa zuwa jam’iyyar ADC. Ya zargi jam’iyyar APC da mamaye PDP, lamarin da ya ce ya tilasta masa sauya sheƙa.
Ya bayyana cewa burinsa yanzu shi ne ƙarfafa sabuwar jam’iyyarsa ta ADC tare da tabbatar da karɓuwarta a wajen matasa da mata a Najeriya.