Rikicin Boko Haram zai tsananta zuwa shekarar 2050 in har ba’a ɗauki mataki ba–Obasanjo

0
61

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, yace daga yanzu zuwa shekarar 2050, za’a samu matsala ta yawan mutane a Nijeriya, inda yawan mutane zai kai miliyan 400, waɗanda za su buƙaci abinci da aikin yi.

Idan muka gaza yin tsari a yanzu, matsalar da za a shiga ta Boko Haram a nan gaba, sai ta ninka wadda ake da ita a yanzu, inji shi.

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi kira da a ɗauki mataki kan matsalar yara miliyan 24 da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan.

Obasanjo ya ce rashin ilimin waɗannan yara na iya zama babban ƙalubale ga makomar Najeriya idan ba a yi abin da ya dace ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Talata a Sokoto, yayin ƙaddamar da cibiyar fasahar sadarwa ta Bakhita ICT Centre.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here