PENGASSAN ta dakatar da yajin aikin da ta shiga

0
37

Kungiyar Ma’aikatan Manyan Jami’an Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta dakatar da yajin aikin da take yi bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya kan rikicin da ya taso tsakaninta da matatar man fetur ta Dangote.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, inda ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan yarjejeniyar da aka cimma.

> “Mun dakatar da yajin aikin, amma za mu yi duba sosai. Idan aka karya wani bangare na yarjejeniyar ko sanarwar ma’aikatar kwadago, ba tare da wani gargadi ba, za mu dawo kan yajin aikin nan take,” in ji shi.

A ranar 26 ga Satumba, kungiyar PENGASSAN ta umurci mambobinta da su shiga yajin aiki na ƙasa saboda korar wasu ma’aikata daga kamfanin ma’adinan mai na Dangote. Sai dai a ranar 1 ga Oktoba, kamfanin Dangote ya amince da sake mayar da ma’aikatan da aka sallama.

Wannan mataki ya kawo ƙarshen zaman dar-dar da masana’antar mai ta shiga sakamakon rikicin, wanda a cewar masana zai iya shafar tattalin arzikin ƙasar idan ya dore.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here