Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar Talata, 1 ga Oktoba, yayin bikin cikar ƙasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
A cikin jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya yi karin haske kan tarihin ƙasar tun daga 1960, zuwa yau yana jaddada cewa, duk da ƙalubale da Najeriya ta fuskanta – irin su yaƙin basasa, mulkin soja da matsalolin tattalin arziƙi – ƙasar ta ci gaba da ɗorewa tare da samun nasarori a fannoni daban-daban.
Ya ce gwamnatin sa ta yi ƙoƙari wajen gyara tattalin arzikin ƙasa ta hanyar kawo sauye-sauye masu tsauri da suka haɗa da cire tallafin man fetur da daidaita tsarin musayar kuɗi. Tinubu ya bayyana cewa, waɗannan matakan sun fara haifar da ɗa mai ido inda ya bayyana cewa kayayyakin da ake samarwa a Najeriya ya haura zuwa kaso 4.23% a watanni 6 na shekarar 2025, sannan hauhawar farashin kaya ya ragu zuwa kashi 20.12% – mafi ƙasa cikin shekaru uku.
Shugaban ƙasa ya lissafo wasu daga cikin muhimman nasarorin da yace gwamnatin sa samu ciki har da:
Ƙarin kuɗaɗen shiga daga haraji da ribar fitar da kaya fiye da shigo da su.
Ƙara adadin ajiyar kuɗin ƙasa a waje zuwa dala biliyan 42.03.
Farfado da masana’antu da noma, da kuma bunƙasa hakar ma’adinai.
Ci gaba da manyan ayyukan gina hanyoyi, jiragen ƙasa da tashoshin jiragen ruwa.
Ƙarfafa shirin tallafin zamantakewa inda aka raba Naira biliyan 330 ga gidaje miliyan takwas.
A bangaren tsaro, Tinubu ya ce dakarun Najeriya na samun gagarumar nasara a yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga, inda ya bayyana cewa, an dawo da zaman lafiya a wasu yankuna da dama musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Ga matasa kuwa, Shugaban ya jaddada cewa su ne ginshikin makomar ƙasa, inda ya ambaci shirye-shiryen tallafi kamar NELFUND na bashi ga ɗalibai, Credicorp da YouthCred domin sauƙaƙa musu rayuwa da kuma shirin iDICE da zai taimaka wajen bunƙasa kirkire-kirkire da fasahar zamani.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi kira da a ƙara daidaita ƙoƙari wajen ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida tare da yin amfani da su, yana mai cewa:
“Mu rungumi ƙasar mu, mu fifita Nigeria a kan komai. Mu haɗa hannu domin tabbatar da sabuwar Najeriya mai cike da fata da bunƙasa.”