Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabiru Yusuf, ya roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sauke kwamishinan ’yan sanda na jihar daga muƙamin sa saboda zargin rashin yin aiki da ƙwarewa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano, a ranar Laraba.
Gwamna Abba ya jaddada cewa, al’umma na buƙatar jami’an tsaro masu gaskiya da adalci, wadanda za su kare rayuka da dukiyoyin jama’a ba tare da nuna son zuciya ba.
An dai yi wannan kira a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan yadda ake gudanar da harkokin tsaro a Kano, musamman kan rawar da rundunar ’yan sanda ke takawa a wasu al’amuran siyasa na jihar.


