Fitaccen malamin Qur’ani kuma masanin ƙira’a a Masallacin Annabi (SAW) da ke Madinah, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya rasu a ranar Laraba bayan kusan shekaru 60 yana koyar da Qur’ani a wannan masallaci mai daraja.
Sheikh Bashir, wanda aka haifa a shekarar 1358 Hijira, ya shafe kusan shekaru 90 a raye, inda ya sadaukar da lokacinsa wajen hidimar Al-Qur’ani da karantar da dubban ɗalibai daga sassa daban-daban na duniya.
Daga cikin malamansa akwai Qari Fath Muhammad Panipati, Sheikh Mahmoud Khalil Al-Husari, da Sheikh Hussein Khattab. Haka kuma, fitattun ɗaliban da ya horar sun haɗa da tsofaffin Limaman Harami – Sheikh Muhammad Ayyoub da Sheikh Ali Jaber, da kuma manyan malamai kamar Sheikh Muhammad Al-Mukhtar Al-Shanqiti, Sheikh Abdul Muhsin Al-Qasim da Sheikh Salah Al-Budair.
Marigayin ya bar babban tarihi a fagen ilimin Qur’ani da ƙira’a, tare da ɗalibai da dama da ke ci gaba da yada wannan ilimi a duniya baki ɗaya.
Allah ya jikan Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya karɓi hidimarsa ga Al-Qur’ani, ya kuma ɗaga darajarsa a cikin bayinsa na salihi.