Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya bayyana cewa wasu gwamnonin jam’iyyun adawa na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Akpabio ya yi wannan bayani ne a Owerri, babban birnin jihar Imo, yayin kaddamar da littafin Gwamna Hope Uzodimma mai taken “Shekaru Goma na Jagoranci Mai Tasiri na Gwamnatin APC a Najeriya”. A wajen bikin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma kaddamar da wasu muhimman ayyuka.
“Shugaban ƙasa, bisa irin abin da kuka cimma a cikin shekaru biyu da suka gabata, ku shirya don tarbar ƙarin gwamnonin adawa,” in ji Akpabio. “Yanzu akwai gwamnoni da dama a Najeriya da ke shirye su koma APC, inji shi.
Ya ƙara da cewa ɗalibai, manoma da ’yan kasuwa sun fara jin daɗin sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta kawo. Akpabio ya kuma yaba wa Gwamna Uzodimma bisa rubuta tarihin aikinsa, yana mai cewa ci gaban jam’iyyar APC na tabbata ne ta ayyuka, ba kawai magana ba.