Fadar shugaban ƙasa ta sanar da cewa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yiwa al’ummar Najeriya jawabi a gobe Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 7 na safe.
Sanarwar, hakan wacce mai bawa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ta ce jawabin na daga cikin bikin tunawa da cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai.
Haka kuma, dukkan gidajen talabijin da na rediyon gwamnati an umarce su da su haɗa kai da tashoshin NTA da FRCN domin watsa jawabin kai tsaye ga jama’a.


