Najeriya a 65: Har yanzu ba mu kai matsayin da ake buƙata ba — Gwamnan Kano

0
62

Najeriya a 65: Har yanzu ba mu kai matsayin da ake buƙata ba — Gwamnan Kano

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa Najeriya tana da nisa wajen cimma burin da ake fata duk da cewa ta cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Gwamnan, wanda shugaban ma’aikatan sa, Dr. Sulaiman Wali, ya wakilta a wajen taron karatun bikin ranar ‘yancin kai da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, ya ce:

“Najeriya a 65 har yanzu tana da nisa daga burin da muke fata. Amma hakan ba abin damuwa ba ne, illa kiran daukar mataki. Dole mu hada kai, mu girmama bambancinmu, mu kuma yi aiki tare don makomar kowa.”

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi gina kasa ta hanyar shiga harkokin dimokiradiyya, tallafa wa tsaro, da kuma bai wa matasa dama ta ci gaba.

Gwamnan ya ce wannan lokacin na cikar shekaru 65 da samun ƴancin kai ya kamata ya kasance ba wai bikin murnar kadai ba, illa lokaci na yin nazari kan yadda shugabanni da jama’a za su taimaka wajen gina kasa mai hadin kai, zaman lafiya da ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here