Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana irin ƙalubalen da ta fuskanta a cocin ta bayan mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin tikitin Musulmi-Misulmi na jam’iyyar APC a zaben 2023.
A sabon littafinta mai suna “The Journey of Grace: Giving Thanks in All Things”, wanda aka wallafa domin cika shekarunta 65, Remi ta bayyana cewa wannan mataki ya raba kan mambobin cocin ta mai suna, Redeemed Christian Church of God (RCCG).
Ta ce duk da cewa ita Kirista ce kuma fasto a RCCG tun daga 2018, hakan bai sa mijinta ya canza ra’ayin tikitin Musulmi-Misulmi ba, abin da ya haddasa rabuwar kai a majami’arta. Duk da haka, ta bayyana cewa ba ta daina zuwa coci ba, kuma ta samu ƙaruwar imani daga ƙalubalen da ta fuskanta.
Remi ta tuna irin irin abin da ya faru a kamfen ɗinta na neman kujerar Sanata a shekarar 2011, inda aka ƙi karɓar takardun tallar kamfen ɗinta a coci. Sai dai ta ce daga baya ta gane cewa coci ba ta da alaƙa da jam’iyya guda, saboda tana da mambobi daga kowane ɓangare na siyasa.
Uwargidan ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin manyan abokan siyasar mijinta sun yi watsi da shi lokacin da ya yanke shawarar yin takara bayan tsawon shekaru 14 yana tunanin hakan. Amma ta ce ta yafe musu, domin ta gane cewa lada daga Allah ne, ba daga mutum ba.