Mulkin Jonathan masifa ne–fadar shugaban ƙasa

0
69

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kaca-kaca da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, kan rade-radin cewa zai tsaya ttakarar shugabancin ƙasa a shekarar 2027, inda ta bayyana mulkinsa na shekaru shida a matsayin masifa ga Najeriya.

A kwanakin baya an samu ƙarin kira daga wasu sassa na ƙasar, musamman daga Arewa, suna roƙon Jonathan da ya dawo ya tsaya takara domin neman canji a zaben 2027.

Wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP kamar tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, da kuma gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, sun fito fili suna kira ga Jonathan da ya shiga takara. Haka kuma, kwanan nan Jonathan ya kai ziyara ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, a gidansa da ke Abuja, abin da ake ganin na da alaka da shirye-shiryen siyasar gaba.

Sai dai a martanin da aka fitar daga fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin, mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa duk da cewa Jonathan na da ‘yancin tsayawa takara, zai fuskanci matsalolin doka da kuma tambayoyi daga al’umma kan cancantarsa.

Onanuga ya yi zargin cewa gwamnatin Jonathan ta yi almubazzaranci, ta gaza tsare dukiyar ƙasa, sannan ta jefa al’umma cikin ƙunci duk da samun kuɗaɗe masu yawa daga mai. Ya ce Jonathan ya karɓi mulki da biliyoyin dala a ajiya amma ya bar gwamnati da ƙarancin kuɗi da bashi mai yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here