Shugaban kwamitin fadar shugaban ƙasa kan gyaran tsarin kuɗi da haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa sabuwar doka ta haraji za ta riƙa karɓar haraji daga wajen mata masu zaman kansu, idan sun samu kuɗi daga sana’ar su.
Oyedele ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a dandalin X a ranar Litinin, inda ya ce dokar haraji ba ta bambance tsakanin abin da ake ɗauka a matsayin halal ko haram ba – abinda take tambaya kawai shi ne: “Ka samu kuɗi daga wata hidima ko kaya? Idan eh, to lallai za ka biya haraji.”
> “Misali, idan mace ta fita ta nemi abokan kwana, ta karɓi kuɗi saboda wannan hidima, kuɗin da ta samu za a ɗora mata haraji a kai,” in ji shi.
Sai dai ya yi bayani cewa kuɗin da ake tura wa dangi, abokai ko ko’ina a matsayin tallafi ko kyauta ba za su shiga cikin haraji ba, domin ana ɗaukar su a matsayin kyauta ba tare da musayar hidima ko kaya ba.
Ya ƙara da cewa wanda ya tura kuɗin ya riga ya biya haraji daga asalin ribar sa, amma wanda aka turawa ba shi da wani ƙarin nauyin biyan haraji.
Wannan sabon tsarin haraji zai fara aiki ne daga 1 ga Janairu, 2026.