Jama’ar Ƙauye Sun Kama ’Yan Bindiga Uku A Katsina

0
63

Al’ummar kauyen Ƙadisau da ke Ƙaramar Hukumar Faskari, Jihar Katsina, sun samu nasarar cafke wasu mutum uku da ake zargin suna da hannu a hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa yankin.

Bayan kama mutanen, mazauna yankin suka mika su ga jami’an tsaron al’umma domin ci gaba da bincike.

Kauyen Ƙadisau da kewaye na daga cikin wuraren da ake yawan kai hare-haren ’yan bindiga, inda aka kashe mutane da dama, aka jikkata wasu da kuma sace dabbobi masu yawa. A wani hari na baya-bayan nan, maharan sun kashe mutane uku, sun yi garkuwa da mata biyar, sannan suka yi awon gaba da dabbobi masu tarin yawa.

Wani bidiyo da aka samu ya nuna jami’an tsaro na tambayar wadanda ake zargin, wadanda suka fito daga kauyukan Ƙadisau, Wasani da Maigora.

Ɗaya daga cikin su ya amsa cewa ya halarci hare-haren da aka kai a Ƙadisau, Unguwar Zango da Kanawa, har ma ya kashe wani mutumi mai suna Mai Soni, saboda ya gane shi. Ya bayyana cewa shi mai safarar makamai ne ga tawagar ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta, wanda ke gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin Maigora da Dajin Birnin Gwari, Jihar Kaduna.

Wani daga cikin wadanda ake zargin ya shaida cewa shi ne ke kai wa wani shugaban ’yan bindiga mai suna Malam kayan abinci da man fetur, kuma ya tabbatar da cewa ya shiga hare-haren da aka kai kauyukan Wasani, Raudama da Unguwar Gizo, inda aka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu.

Na ukun kuma ya bayyana cewa yana kai kayan abinci, man fetur da wasu buƙatu ga wani shugaban ’yan bindiga mai suna Auwali, wanda yake da alaka da Malam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here