Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi kira ga sauran gwamnonin Arewa da su ɗauki cikakken nauyin tsaron jihohinsu, yana mai cewa yanzu babu wata hujja ta gaza ɗaukar mataki ganin cewa kuɗaɗen da ake rabawa daga Abuja sun ninka fiye da na baya.
Ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.
Sule ya ce a yanzu duk matakan gwamnati suna samun kuɗaɗe masu yawa fiye da duk wani lokaci a baya, inda aka raba sama da naira tiriliyan biyu da miliyan dari biyu ga gwamnati a wannan watan.
> “Duk wata jiha yanzu tana da isassun kuɗaɗe don kare jama’arta. Bai kamata mu riƙa zargin wani kan matsalar tsaro ba. Idan akwai wanda ya kamata a zarga, to mu gwamnonin jihohi ne,” in ji shi.