Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da raba tallafin farko na shirin inganta rayuwar matasa domin ƙarfafa gwiwar masu sana’o’i da ƙananan ’yan kasuwa a jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Talata, sama da matasa 5,384 – maza da mata – sun samu tallafin naira 150,000 kowannensu, wanda jimillar kuɗin ta kai naira 800,700,000.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da shirin, Gwamna Yusuf ya ce wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnatinsa na inganta rayuwar matasa da kuma ba su damar taka rawar gani a harkokin kasuwanci.
Ya yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin wajen bunƙasa harkokinsu, domin tabbatar da kyakkyawar makoma.
Haka kuma, gwamnan ya roƙi waɗanda suke kan jerin masu jiran samun tallafin da su yi haƙuri, yana mai tabbatar musu cewa za a fitar da kaso na biyu na shirin nan ba da jimawa ba.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa matasa muhimmanci ta hanyar manufofi da shirye-shiryen da za su samar musu da hanyoyin dogaro da kai da kuma ɗorewar tattalin arziki a Kano.