Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, reshen jihar Kano, ta bayyana shirinta na ƙara haɗin kai da ƴan jarida, musamman wakilan kafafen yaɗa labarai na ƙungiyar NUJ, domin samun nasara a yaƙi da cin hanci da aikata laifukan tattalin arziƙi.
Mukaddashin Daraktan Hukumar a Kano, Sa’ad Hanafi Sa’ad, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi tawagar shugabannin ƴan jaridar a hedikwatar hukumar da ke Kano.
Sa’ad ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawar takawa a yaƙin da ake yi da rashawa, domin su ne ginshikin wayar da kai, fallasa cin hanci, da kuma tabbatar da gaskiya.
“Ina matuƙar jin daɗin wannan ziyara. Ina kira gare ku da ku haɗa hannu da mu a wannan yaƙi da laifukan tattalin arziƙi. Ƙofofin hukumar mu a buɗe suke gare ku, ko da akwai lokacin da suka rufe, yanzu an buɗe su baki ɗaya,” in ji shi.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar ƴan jarida wakilan kafafen yaɗa labarai na Kano, Murtala Adewale, ya yaba da ƙoƙarin EFCC wajen yaƙi da cin hanci, duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Ya nemi ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar da ƴan jarida, musamman ta hanyar shirya horaswa akai-akai domin ƙara ƙwarewa.
Adewale ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da EFCC zai ƙara ƙarfafa yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa a Najeriya.