DSS ta gurfanar da Sowore bisa zargin aibata shugaban ƙasa Tinubu

0
67

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ya aibata shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a shafinsa na X.

Baya ga Sowore, hukumar ta kuma gurfanar da manyan kamfanonin sada zumunta — X da Meta — bisa zargin ƙin bin umarninta na goge rubuce-rubucen da ta kira kalaman ƙarya da cin mutunci ga shugaba Tinubu.

Tun a ranar 6 ga watan Satumba, DSS ta nemi a dakatar da shafin Sowore a X, tana mai cewa wallafe-wallafensa na iya tayar da fitina da kuma barazana ga tsaron ƙasa. Hukumar ta ce matakin ya zama dole domin kare martabar shugabanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a ƙasa.

Sai dai, har yanzu X bai goge ko kuma rufe shafin Sowore ba, lamarin da DSS ta ce ya sa ta ɗauki matakin gurfanar da kamfanin a kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here