Dakarun sojin Najeriya a karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar cafke wani soja da kuma ɗan sanda bisa zargin hannu a safarar makamai da kayan yaƙi zuwa ga ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabas.
Rahotonni sun bayyana cewa an gudanar da kamen ne tsakanin ranar 26 zuwa 28 ga Satumba, bayan samun bayanan sirri kan wasu makamai da ake jigilar su ta wata hanya da ake amfani da ita wajen kai wa ‘yan ta’adda kayan yaƙi a Borno.
An kama su da bindigogi, harsasai da na’urorin sadarwa, waɗanda suka tabbatar da alaka tsakaninsu da wata babbar hanyar safarar makamai da ake ci gaba da bincike a kanta. Yanzu haka suna hannun sojoji inda ake musu tambayoyi kafin mika su kotu.
Baya ga hakan, dakarun sun kuma cafke wani da ake zargi da haɗin guiwa da Boko Haram a Baga (Borno), tare da kwace babura uku da lita 32 na man fetur a Mubi (Adamawa). A Kankara (Katsina), an kama wani mai taimaka wa ‘yan ta’adda wajen jigilar kayayyaki da kuma leƙen asiri da ake zargin yana hulɗa da dillalin makamai.
Haka kuma, an samu damar ceto wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su, koda yake wani daga cikin masu laifin ya tsere lokacin da ake shirin kama shi.
Hedikwatar tsaro ta bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba wajen murƙushe haɗin kai na cikin gida da ke taimaka wa ta’addanci da kuma dakile hanyoyin samun makamai ga ‘yan ta’adda.


